AREWA: Gwamnonin Arewacin Najeriya sun bayyana alhinin su matuƙa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa da mai bayar da tallafi, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar da wannan saƙon ta’aziyya a madadin sauran gwamnonin Arewa, inda ya bayyana rasuwar Aminu Dantata a matsayin babban rashi ga ƙasa da kuma ƙarshen wani zamani mai albarka.
A cikin wata sanarwa daga Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce:
“Cike da alhini da jin nauyin rashi, a madadin al’ummar Jihar Gombe da Gwamnonin Jihohin Arewa baki ɗaya, muna alhinin rasuwar babban dattijo, jarumi a harkar kasuwanci, kuma mai taimako na gaskiya, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Wannan mutuwa ta kawo ƙarshen wani zamani mai albarka — zamani na hangen nesa, karamci ba tare da iyaka ba, tawali’u da gaskiya.”
Gwamnan ya bayyana Alhaji Aminu Dantata a matsayin babban ginshiƙi a tarihin tattalin arzikin Najeriya, wanda rayuwarsa ta nuna nagarta da sadaukarwa ga ci gaban al’umma.
“Gudunmawar da Alhaji Aminu Dantata ya bayar wajen ci gaban Arewacin Najeriya da ƙasar gabaɗaya abin alfahari ne. Mun rasa wani tsoho mai ba da shawara, wanda duk lokacin da ya buɗe baki sai ka ji daraja da hikima,” in ji shi.
Ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Dantata, Gwamnatin da al’ummar Jihar Kano, da kuma Najeriya baki ɗaya. Ya kuma roƙi Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya karɓe shi cikin rahamarSa, ya kuma sa Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.
English-
📝 Rahoton Arewa News Flash

No comments:
Post a Comment