Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, wato NNPC Limited, ya fitar da wani bayani mai zafi inda ya bayyana cewa wasu mutane na ciki da wajen kamfanin sun haɗa kai domin ɓata sunan shugabanci da dakile sauye-sauyen da ake ƙoƙarin aiwatarwa a kamfanin.
A cikin sanarwar da hukumar gudanarwar kamfanin ta fitar a ranar Juma’a, an zargi wata ƙungiya da yaɗa ƙarya da bayanan bogi da nufin yaudara da karkatar da hankalin jama’a.
Kamfanin ya bayyana cewa an shirya wani shiri mai zurfi na ɓata suna da kawo cikas ga gyare-gyaren da ake yi a kamfanin, tare da ƙoƙarin karya gwiwar ma’aikata da masu kishin ci gaban Najeriya.
“Wasu daga cikin dabarunsu sun haɗa da wallafa rahotannin ƙarya da sunan almundahana, domin karkatar da shugabanni, yaudara al’umma, da hana ma’aikata da ’yan Najeriya masu kishin ƙasa cigaba da jajircewa,” in ji sanarwar.
Kamfanin ya ƙara da cewa waɗanda ke shirya wannan abu su ne waɗanda ke jin tsoron gaskiya, sauyi da nuna amana a tsarin aiki.
“Waɗannan shirye-shiryen makirci alama ce ta tsoro daga waɗanda ke ƙoƙarin hana gaskiya da sauyi. Sun nuna matakin da za su iya zuwa domin hana sabuntawar da NNPC ke yi.”
NNPC ta yi kira ga ma’aikatanta, abokan hulɗa da ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su ƙarfafa guiwa, su kau da kai daga hayaniyar da ke yawo, kuma su ci gaba da mara wa sabbin sauye-sauyen baya.
English translation:
The Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) has raised an alarm over what it describes as a well-coordinated sabotage campaign aimed at undermining its leadership and halting its ongoing transformation agenda.
In a strongly worded statement released on Friday, the company alleged that a syndicate — both within and outside the organisation — is behind the deliberate spread of misinformation and false narratives.
NNPCL said the attacks are part of a broader plot to derail its reform process, damage the image of its leadership, and discourage the commitment of patriotic Nigerians within the sector.
“Their tactics include planting scandalous and fabricated reports, curated to distract leadership, mislead the public, and undermine the commitment of our dedicated workforce and reform-minded Nigerians,” the statement read.
The company further stated that the orchestrated attacks are clear evidence of resistance from individuals and groups who feel threatened by the push for transparency, accountability, and institutional reform.
“These are calculated efforts by those who feel threatened by reform, transparency, accountability, and change. It shows the extent they’re willing to go to stop the transformation of Nigeria’s foremost energy institution.”
NNPCL urged its staff, stakeholders, and Nigerians at large to remain focused and not be distracted by what it described as “the noise.”

No comments:
Post a Comment