Peter Obi Ya Yabi Murabus ɗin Ganduje a Matsayin Shugaban APC na Ƙasa- English - Obi hails Ganduje’s resignation as APC chairman. Peter Obi Ya Yabi Murabus ɗin Ganduje a Matsayin Shugaban APC


 Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya bayyana gamsuwa da yanda tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC a matakin ƙasa.

Ganduje ya miƙa wasikar murabus ɗinsa ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta hannun Sakatare na Ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, a ranar Jumma’a. Ya ce dalilin haka shi ne wasu ƙalubale na lafiya da ya ke fuskanta.

Peter Obi ya mayar da martani a shafinsa na X (wanda a da ake kira Twitter) inda ya bayyana cewa matakin da Ganduje ya ɗauka alama ce ta girman kai da fahimtar abinda ya dace da shi.

“Ina fatan labarin da na karanta gaskiya ne cewa Ganduje ya ajiye mukaminsa saboda dalilan lafiya. Idan haka ne, na yaba da matakin. Wannan babban misali ne na jagoranci,” in ji Obi.

Wasu daga cikin ’yan siyasa da jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan murabus, amma sakon Peter Obi ya ja hankali sosai saboda yana ɗauke da girmamawa da kishin juna.

📝 Arewa News Flash ta kawo muku wannan rahoto.


English Translation 


The 2023 Labour Party presidential candidate, Mr. Peter Obi, has publicly commended Dr. Abdullahi Umar Ganduje for resigning from his position as the National Chairman of the All Progressives Congress (APC).

Ganduje, a former Governor of Kano State, tendered his resignation through the National Secretary of the APC, Senator Ajibola Bashiru, on Friday, citing health-related reasons for his decision.

Reacting to the development via his official X handle (formerly Twitter), Peter Obi described the move as a bold and thoughtful step, saying it reflects leadership and maturity.

“I have just read reports that Dr. Ganduje has stepped down as APC National Chairman, citing health challenges. If this is true, I commend him for prioritising his health. That in itself is leadership,” Obi wrote.

Ganduje’s resignation has generated varied reactions across the political space, but Obi’s message stands out as a rare gesture of political civility.

📝 Filed by Arewa News Flash

No comments:

Post a Comment