ABUJA – Juma’a, 27 ga Yuni, 2025
A cikin wani sakon da ya cika da albarka da nufin tunatar da al’umma muhimmancin addu’a da salati ga Annabi Muhammad (S.A.W), Hon. Abdullahi Tanko Yakasai, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan hulɗa da al’umma (yankin Arewa maso Yamma), ya fitar da saƙon musamman a safiyar wannan Juma’a mai albarka.
Ya rubuta kamar haka:
“Tsira da Aminci Ya Allah Ka ƙarashi ga Shugaban Halitta (S.A.W).”
“Ya Allah (S.W.T) kasadamu da dukkan alkhairan wannan rana mai albarka.”
Wannan saƙon ya zo daidai da Juma’ar da Musulmai ke amfani da ita wajen yin salati da addu’a ga Manzon Allah, da kuma rokon rahama da alkhairi daga Ubangiji.
Hon. Tanko Yakasai, wanda aka sani da kasancewa cikin jama’a da karɓuwa a yankin Arewa, ya rinka wallafa irin wannan tunatarwa a kai a kai domin gina ruhin zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kai da kuma karfafa al’umma su rungumi kyawawan dabi’u da tunani mai kyau.
Sakon ya karade dandalan sada zumunta tare da fatan alheri daga magoya baya da jama’a daga sassa daban-daban na ƙasa.
“Juma’at Kareem ga daukacin Musulmai, muna rokon Allah ya amsa dukkan addu’o’inmu,” in ji wani daga cikin masu bibiyar saƙon nasa.

No comments:
Post a Comment