Tinubu Ya Hada Wike da Fubara Kan Teburin Sulhu – BBC AUSA Ta Fito Da Labari Safiyar Yau - Tinubu Reconciles Wike and Fubara – “We’re Brothers, It’s All in the Past” – They Say

 

ABUJA — Safiyar yau, BBC AUSA ta wallafa cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kafa zaman lafiya tsakanin tsohon Gwamna na jihar Ribas kuma Ministan Abuja yanzu, Nyesom Wike, da gwamnan yanzu na jihar, Siminalayi Fubara.

Tun kafin wannan rana, lamarin ya kankama sosai. Wike da Fubara sun shafe watanni suna ragargaza juna a kafafen gwamnati, har aka kai ga ayyana dokar ta-ɓaci da dakatar da Fubara daga mulki na tsawon wata shida – abin da ya gigita siyasar Ribas gaba ɗaya.

Amma yau komai ya sauya.

A lokacin zaman sulhu da aka yi a fadar shugaban ƙasa, Wike ya ce:

"Komai ya wuce. Mun amince mu ci gaba da aiki tare, domin mu 'yan uwa ne."

Shi kuma Gwamna Fubara bai tsaya a baya ba, ya ce:

"Abin da muke bukata a Ribas yanzu shine zaman lafiya. Kuma za mu yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da hakan."

Hoton da aka fitar daga fadar gwamnatin Najeriya ya nuna su duka cikin dariya da musabaha kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa.

Wannan sulhu na zuwa ne bayan cece-kuce da yawa daga jama’a, kafafen yada labarai da kuma ‘yan siyasa da ke kallo daga nesa suna jira yadda lamarin zai kaya.

Masu sharhi na ganin cewa wannan sulhu da Tinubu ya yi ba kawai domin kwantar da hankali ba ne, har ma domin ceto jam’iyyar APC daga durkushewa a kudu maso kudu.




🔴 Reporting by: Ariwa News Flash



No comments:

Post a Comment